Script 1
[Za’a yi amfani da wannan rikodin a bidiyon samfurin mu. Muna bukatan sautin yayi karfi, ya bada sha’awa kuma ya fita cikin kwarewa] Me yasa muka zama mafi kyawun zaɓin ƙwararrun yan rikodin murya?
Da farko, muna isar da fitattun rikodin murya ne kawai waɗanda ƙungiyar Kula da Ingancin mu ta tantance. Bayan haka, muna da masu rikodin murya dubunnai na duk wani yaren da kake so, salo da farashi mai dacewa! Bayan nan, ayyukanmu suna ƙarƙashin garantin gamsuwa, idan baka gamsu da sakamakon ba, ƙungiyar sarrafa kayan aikin mu zata shiga ciki ta maida maka da kuɗin ka. [Ka ɗan dakata bayan kowace kalma] Babu yawan tambayoyi
Mu masu tsattsauran ra'ayi ne game da tallafin abokan ciniki; ƙungiyarmu tana farin cikin taimakawa. Zamu tabbatar da cewa zaman ka da mu babu matsala, cikin ƙwarewa, [Ka ɗan dakata a nan] kuma mai daɗi!
Script 2
[Za’a yi amfani da wannan rikodin a cikin bidiyon tallan mu. Muna buƙatar ya fita cikin sautin almara, ban sha’awa kuma ya dan ba da mamaki.]
A duniyar da masu rikodin murya ke da wuyan samu. A duniyar da ke da wahala da tsadar sana'ar rikodin murya, mun yanke shawarar fara juyin juya hali! Tafiyar bata kasance mai sauƙi ba, amma mun yi ƙarfi fiye da da.
Mataki-mataki, mun ƙirƙiri sabis na dijital domin kawo maka masana'antar rikodin murya har gida. Mun saka ka a cikin wannan manufa kuma muna tsammanin zaka shiga cikin wannan tafiya.
Babu waiwaye.
Mun zo, mun canza duniya, kuma muna nan [Ka ɗan dakata a nan] zaune.
Zamu kawo masana'antar rikodin murya a hannunka.